KANNYWOOD: ZAN DAINA RAWA DA WAKA A FILM – INJI ALI NUHU

Shahararren dan wasan Kwaikwayo

na Kannywood Ali Nuhu wanda aka fi

sani da Sarkin Kannywood ya bayyana

ma BBC Hausa cewa ya kusa daina

rawa da waka, amma fa sai idan lokaci

yayi.

Sarki Ali yace sau dayawa ya kan yi

rawa da waka ne kadai idan hakan ya

zama dole, musamman idan Fim din

na bukatar ayi hakan.

Sarki Ali ya kara shaida ma majiyar

HAUSATOP cewar idan da za’a

kwatan ta irin rawar da yake yi a baya,

za’a gane cewa ya rage sosai.

Sai dai jarumin Fim din Hausan,

wanda a yanzu shekarunsa 44 bai

bayyana yaushe ne ranar da zai daina

yin rawa ba. A wani hannun kuma a

kwanan nan ne Ali Nuhu ya fitar da

sabon Fim dinsa Mansoor, wanda

masana suke ganin ya kawo sabon

salo a Kannywood.​

Leave a Response