logoHOME
Home
music
Music
videos
Videos
gists
Gists
Tags:
Website Design

« | »

NEWS: RAHMA SADAU ZATA GANA DA PRIYANKA CHOPRA


Fitacciyar Jarumar Masana’antar shirya Fina-finan Bollywood Priyanka Chopra na fatan haduwa da Jarumar Fina-finan Hausa ta Kannywood Rahama Sadau a dan wani lokaci kadan mai zuwa.

Tun farko Jaruma Rahama Sadau ce ta aika da sakon bankadar mafarkinta a fejin Priyanka na Twitter kan irin mafarkin da take da shi na kasancewa kamar Jaruma Chopra. Sakon wanda Jarumar ta rubuta kamar haka “Idan na duba nasarar da kika cimma, tana bani karin gwiwa na zama kamarki” – inji Sadau zuwa ga Chopra.

Sadau ta samu amsar kalmominta ‘yan dakikoki kadan daga Chopra wadda ta ba ta alwashin cewar “Ina godiya Rahama Sadau. Ina Fatan haduwa da ke nan gaba. Fatan alheri da kauna kan komai” – Inji Jaruma Priyanka Chopra.

Jaruma Sadau ta nuna murnarta matuka kan samun wannan amsa tare da ayyana cewar tana nan tana jiran lokaci. Sadau dai ta dade da kaunar wannan jaruma a ranta, wanda har ta kai ana mata lakabi da sunan Jarumar wato Priyanka Chopra ta Kannywood.

Written by: admin muryararewa.com

Share This With Your Friends

AREWATUNES Content Copyright Content Copyright: Please do not cut, copy or lift this page content without our concern. Images posted are believed to be published according to the U.S Copyright Fair Use Act (title 17, U.S. Code.).
AREWATUNES Content Removal Content Removal: If you believe that this page has violated your copyrighted/protected material(s), please kindly Contact Us Here for immediate removal, or mail us at yourmail@gmail.com stating the content name/URL of the page. Thanks, AREWATUNES (c)

Tags: , , ,

Categories: Kannywood, News

Season Greetings
Season Greetings

0 Responses

Leave a Reply

« | »