Fitaccen mawakin Hausa, Hussaini Danko, ya dawo da sabon salo a cikin wakarsa mai taken “Gargajiyar Mu”. Wannan waka, wacce aka fitar a ranar 28 ga Mayu, 2024, tana alfahari da al’adunmu na Hausa, tana kuma cike da sakonni masu zurfi game da kishin gargajiya da al’adu.
Wakar ta samu karɓuwa sosai a cikin ‘yan kwanaki, inda ta ke jan hankalin masoya wakokin Hausa. Zaku iya sauraron wannan waka kai tsaye a YouTube ta hanyar wannan haɗin: Gargajiyar Mu – Hussaini Danko.
Ku saurara, ku ji yadda Hussaini Danko ya tsage gaskiyar gargajiyar mu cikin salo mai kayatarwa!